IQNA

Muhimman Abubuwan Da Suka Faru A Kasar Iraki

17:32 - July 26, 2014
Lambar Labari: 1433626
Bangaren kasa da kasa, a cikin 'yan makonnin abubuwa da dama sun faru a Iraki masu ban takaici daga bangaren 'yan ta'adda na kungiyar takfiriyya wanda hakan ya san al'ummomin duniya yin Allawadai da abin da suka yi.

Jerin hare-haren ta’addanci ta hanyar tarwatsa motoci da aka makare da bama-bamai a sassa daban daban na birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki sun lashe rayukan mutane akalla ashirin da uku tare da jikkata wasu sabain da hudu na daban.
Majiyar tsaron Iraki ta bayyana cewa; Jerin hare-haren ta’addancin da aka kai a yankuna hudu da suke birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki ta hanyar tarwatsa motoci da aka makare da bama-bamai sun yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla ashirin da uku tare da jikkata wasu fiye da 74 na daban.
Majiyar ta kara da cewa; Tarwatsewar motoci biyu a yankunan Baya’a da Saidiyya da suke kudancin birnin Bagadaza sun lashe rayukan mutane akalla 6 tare da jikkata wasu 33 na daban, baya ga hasarar dukiyoyin jama’a. Sannan harin kunan bakin wake a yankin Abu-Dashir ya lashe rayukan mutane 8 tare da raunata wasu na daban. Haka nan harin kunan bakin wake ya lashe rayukan mutane tara  tare da jikkata wasu kimanin ashirin na daban a yankin Kazimiyya da ke arewacin birnin na Bagadaza.
Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta duniya ta sanar da cewa; Kungiyar ta’addanci ta daular Musulunci a Iraki da Sham wato Da’ish tana ci gaba da aiwatar da kashe-kashen gilla a garin Mosel na kasar Iraki da ta mamaye.
A rahoton da Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta fitar a yau Litinin ta bayyana cewa; ‘Yan kungiyar ta’addanci ta daular Musulunci a Iraki da Sham wato Da’ish da suka mamaye garin Mosel gari na biyu mafi girma a Iraki da wasu yankunan da suke arewacin kasar suna ci gaba da aiwatar da kashe-kashen gilla kan jama’a tare da kame mutanen da suke kokarin tserewa daga yankunan da suka mamaye.
Har ila yau rahoton ya kara da cewa; Dubban daruruwan mutane ne suka fice daga garin na Mosel domin tsira da rayuwarsu daga kashe-kashen gillar ‘yan kungiyar Da’ish da kuma tsoro hare-haren jiragen saman yaki sojin gwamnatin Iraki a kokarin da suke yi na kwace garin daga hannun ‘yan ta’adda.
1433005

Abubuwan Da Ya Shafa: Irak
captcha