Shugaban na jamhuriyar Musulunci ya yi kira da a kawo karshen zubar da jnin al’ummar Palasdinu da h.k. Isra’ila ta ke yi da kuma duake takunkunin da aka kakabawa yankin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, bugu da kari shugaban kasar Iran din ya zargi h.k. Isra’ila da yi wa palasdinawa kisan kiyashi. Shi kuwa ministan harkokin wajen Palasdinu .. ya yi Allah wadai ne da gajiyawar kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wajen kawo karshen zubar da jinin al’ummar Gaza.
Ya kuma ci gaba da cewa za su kwankwasa kofar kowace kungiya ta kasa da kasa domin takawa h.k. Isra’ila birki. Bayanin bayan taron ya amince da shawarar da ministan harkokin wajen kasar Lebanon ya gabatar na kai karar h.k. Isra’ila a gaban kotun manyan laifuka ta kasa da kasa.
Wannan dais hi ne karo na farko dacwannan kwamiti ya gudanar da zamansa tun bayan da haramyacciyar kasar Isra'ila ta fara kaddamar da hare-haren bayanan a kan fararen hula a yankin Gaza.
1435614