Wannan hari ya zo ne kasa da sa'oi 24 da kai wani makamancinsa da 'yan ta'addan na ISIS suka yi a birnin Bagadaza, inda a nan ma suka kashe fararen hula fiye da 50 tare da jikkata daruruwa.
Mayakan kungiyar ISIS da ke samun goyon bayan Amurka, Saudiyyah, Turkiya da kuma Isra'ila, sun kwace iko da wasu kauyukan kurdawa da ke kusa da garin Mausil, amma mayakan Kurdawa tare da taimakon jiragen yakin kasar Iraki sun samun nasarar fatattakar 'yan ta'addan na ISIS, duk kuwa da cewa dubban daruruwan mutane mazauna kauyukan sun kaurace ma yankunansu.
A bangare guda kuma 'yan ta'addan na ISIS sun sanar da cewa sun fara sayar da matan da suka kame kuma suke garkuwa da su a garin Mausil a matsayin bayi, yayin kwamandoji daga cikinsu suke zabar wadanda suka yi musu a matsayin kuyangi.
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da ayyukan ta’adancin da kungiyar daular Musulunci a Iraki da Sham wato Da’ish ke aiwatarwa a kasar Iraki.
A bayanin da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fitar bayan rattaba hannun dukkanin mambobinsa ya yi tofin Allah tsine kan irin ayyukan ta’addanci da ‘yan kungiyar Da’ish suke gudanarwa kan mabiya ‘yan tsirarun addinai a kasar Iraki tare da bayyana ayyukan na ‘yan kungiyar Da’ish da cewa cin zarafin bil- Adama ne tsantsa.
Har ila yau kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana tsananin damuwarsa kan yadda ayyukan ta’addancin kungiyar Da’ish suka tilastawa dubban daruruwan Irakawa yin gudun hijira, don haka ya bukaci dukkanin al’ummun kasar ta Iraki da su hada kai waje guda domin yakar masifar kungiyar ta’addanci ta Da’ish.
Mayakan kungiyar ta’addanci ta daular Musulunci a Iraki da Sham wato Da’ish dai suna ci gaba da kashe al’ummar musulmi ‘yan shi’a gami ‘yan sunni da suke adawa da ayyukan ta’addancinsu da kuma sauran mabiya addinai da bana Musulunci ba tare da yin fyade ga matansu a matsayin bayi.
1436961