IQNA

Ban Ki Moon Ya Bukaci A Kara Wa'adin Tsagaita Bude Wuta A Gaza

23:53 - August 11, 2014
Lambar Labari: 1438358
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren majalisar dinkin duniya ya bukaci da a kara tsawaita lokacin dakatar da bude wuta a yakin da ake yi a Gaza wanda yahudawan sahyuniya suke kashe mata da kananan yara.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, Ban Ki Moon babban sakataren majalisar dinkin duniya ya bukaci da a kara tsawaita lokacin dakatar da bude wuta a yakin da ake yi a Gaza wanda yahudawan sahyuniya suke aikata ta'asa tare da cikakken gon bayan uwayen gidansu.
Al'ummar Palstinu na ci gaba da bayyana farin cikinsu dangane da nasarorin da mayakan gwagwarmaya suka samu kan haramcecciyar kasar Isra'ila.   Yayin da bangarorin biyu ke ci gaba da tattaunawar dakatar da buda wuta na din-din a kasar Masar, Al'ummar Palstinu na bayyana fara'arsu  kan irin nasarorin da kungiyoyin gwagwarmaya suka samu kan h k isra'ila.
A daren jiya Talata khalid Albatash daya daga cikin shugabanin kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul islam ya bayyana cewa Al'ummar Palastinu tare da mayakan gwagwarmaya sun karya lagon Gwamnatin sahayoniya wacce take babbar makiya ce ga Al'ummar Palastinu baki daya kuma Siyasar Sojojin Sayoniya na rusa kungiyoyin gwagwarmaya ba zai ci nasara ba har abada
Albatash ya ce har abada ba za su amince ba da wata yarjejjeniya wacee za ta cutawa Al'ummar Palastinu don haka idan ana bukatar cimma yarjejjeniyar din din din to wajibi a kawo karshen takunkumin da aka sanyawa Al'ummar zirin Gaza na tsahon shekaru 8.
Daga nashi waje Sa'ib Uraikat daya daga cikin wakilan Palastinawa a tattaunawar birnin Alkahira ya ce manufar harin da HKI ta kai zirin Gaza sake kwace wani bangaren yankin Palastinu amma har abada Palastinawa ba za su bada damar tabbatar da mafalkin Isra'ilan ba sannan ya kamata Duniya ta sani lokaci yayi da za kafa kasar Palastinu a matsayin kasa mai cikekken 'yanci.

1437100

Abubuwan Da Ya Shafa: Ban
captcha