IQNA

Nuna Rashin Amincewa Da Buga Kur'ani Mai Kure A Kasar Algeriya

22:02 - August 13, 2014
Lambar Labari: 1439209
Bangaren kasa da kasa, an nuna rashin amincewa da buga wani kwafin kur'ani mai tsarki da ke da kure a cikin bugun nasa akasar Algeria wanda daga bisani aka an kara tare da yin kira da a kawar da wannan kwafi.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa an yanar gizo na sharq online cewa, musulmi da dama suna nuna rashin amincewa da buga wani kwafin kur'ani mai tsarki da ke da kure a cikin bugun nasa a kasar Algeria wanda daga bisani aka an kara tare da yin kira da a kawar da wannan kwafin wanda yake yawo a hannun mutane a halin yanzu.

A cewar wani daga cikin makarantan kur'ani nakasar an buga kur'ani ne  a cikin shekara ta 2003, kuma yana cikin salon kira'a ne ta Warsh, daga cikin shafukan da ke da matasala akwai 389 da kuma 392, a cikin aya ta 35 da kuma 51  a cikin surat Kisas.

Sai kuma ayoyi na 15 da 18  da kuma aya ta 11 a cikin surat Sajdah, sai kuma 416 da 417 da kuma 411, wadanda dukakninsu suna daga cikin shafukan da aka samu kura-kurai masu yawa, wadanda suka sabawa a bin dake cikin kur'ani wanda kuma mai karantawa zai rika karantawa da kure, akan aka bukaci da janye wadannan kafofi na kur'ani mai kure baki daya.

1438488

Abubuwan Da Ya Shafa: algeria
captcha