Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa, a cikin wannan mako ne aka gudanar da wani zaman taro na makon al’adun muslunci da kuma na Iran da suka shafi musulunci da aka saba gudanrwa a kasar Tunisia tare da halartar jami’ai na kasar ta Tunisia da kuma jami’an huldar diplomasiyya na kasar Iran da ke birnin Tunsia.
Babbar manufar wannan taron dai ita kara dangon alaka da zumunci tsakanin al’ummomin kasashen biyu wadanda suke da madaukakin matsayi a cikin al’du da kuma ci gabana ddinin muslunci, sakamakon rawar da suka taka tsawon shekaru na tarihin musulunci, wanda hakan ya sanya su a sahun gaba wajen bayyana irin wadannan al’adu da suk danganci addinin muslunci.
Yanzu haka dai an kamala taron tare da fitar da bayani da ke karfafa muhimmancin ci gabansa akowace shekara, domin karuwar al’ummomin kasashen biyu ad suke da dadddiyar alaka ta tarihi, haka nan kuma an jaddada wajabcin bayar da muhimmanci ga hadin kan musulmi a duk inda suke.
1439668