Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islam.ru masu kula da aikin hajji sun tabbatar da cewa bayan kammala aikin hajjin bana wasu daga cikin maniyyata za su ziyarci wani dogon bene da mahukuntan Saudiyya suka gina wanda kuma hakan ya ke ci gaba da jawo rikici tsakanin 'yan kasar da ma wasu daga wajenta.
An dai gina wannan bene a cikin wani fili wanda yake tattare da masallacin haramin ka'abah wanda ya kasance daga wani bangare da zai iya rufe masallacin ba za a ganshi ba, wanda hakan ya sa ake kallon wannan a matsayin wani shiri na batar da alamomin tarihi da addini da ke wurin.
Yanzu haka dai an saka agogo a kan benen a mtsayin wani wuri da zai rika alamata birnin Makka maimakon dakin ka'abah mai alfarma wanda shi en asalin birnin.
1440343