Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-dastur ta kasar Jordan cewa, shekh Zaglul Al-najjar daya daga cikin fitattun masana kur'ani kuma makaranta a kasar Masar ya bayyana cewa komawa zuwa ga kur'ani mai tsarki tare da fahimtar ma'anoninsa hakan shi ne mafita ga matsalolin da musulmi suke fuskanta a wanann zamani da suka shiga dimuwa da rashin sanin ina suka nufa.
Malamin ya ci gaba da cewa Allah madaukakin sarki ya sanya kur'ani ya zama shi ne fitila mai haskakawa ga musulmi a kowane lokaci, kuma wannan bai takaita da lokacin manzo ba kawai, a duk lokacin da msuulmi suka shiga wani fangima to su koma ga kur'ani su fahimci koyarwa to babu shakka za su samu mafita daga matsalolinsu.
Da dama daga cikin makaranta a kaar Masar suna bayar da muhimamnci matuka wajen karatu tare da sanin manonin ayoyi domin ya zama sun samu ilimin karatu da kuma sanin ma'anonin ayoyi bisa ga bayanin malamai da suke komawa zwa gare su a cikin lamurransu na addini.
Kasar Masar dai it ace kasa ta farko wajen yaye makarnta da mardata kur'ani mai tsarki a tsakanin dukaknin kasashen musulmi na duniya baki daya.