Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Nas cewa, dakin littafan Saudiyyah zai rarraba kwafin kur’ani mai tsarki ga mahalrta taron baje kolin littafai na kasa da kasa da a za afara gudanarwa daga daren yau a fadar mulkin kasar kamar yadda aka saba a kowace shekara.
Bayanin ya ce a yau ne za a gudanar da taron bude baje kolin na litatfaii wanda zai samu halartar madabantu daga kasashen musulmi da na larabawa daban-daban domin nuna irin littafan da suke bugawa na addini domin sayar da su ga masu nazari da kuma wadanda ake bugawa domin amfabnin makarantu.
Dakkin littafan Saudiyya yana dauke da littafai kimanin dbu 25 da kuma kwafin kur’ani mai tsarki guda dubu 5 wadanda duk za a raba su ga mahalrta taron baje kolin, wanda zai dauki tsawon kwanaki 11 ana gudanar da shi.
1445417