IQNA

Za A Kara Yawan Sa’oin Watsa Shirin Kur’ani A Gidajen Radio Na Aljeriya

7:22 - September 07, 2014
Lambar Labari: 1447329
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Aljeriya sun bayar da umarnin kara yawan sa’oin da ake gudanar da shirin kur’ani mai tsarkia gidajen radiyon kasar da nufin bunkasa harkokin da suka shafi karatu da koyar da ilmomin kur’ani a kasar.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna yanakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na gidan radiyon Algiers cewa a kasar Aljeriya sun bayar da umarnin kara yawan sa’oin da ake gudanar da shirin kur’ani mai tsarkia  gidajen radiyon kasar da nufin bunkasa harkokin karatu da koyar da ilmomin kur’ani ta hanyar gidajen radiyo, shirin zai rika gudana a kan AM daidai mita 1422 kilo htz, sai kuma kan FM kilo htz 104.2، 101.5 da kuma 95.6.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu hakan zai taimaka matuka wajen kara yawan fadada ilmantarwa ga a’ummar kasar ta fuskar kur’ani mai tsarki, domin kuwa za a yi amfani da salon a zamani wajen bunkasa wadannan shirye-shirye kamar dai yadda bayanain ma’aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar ta sanar dangane da hakan.
Aljeriya tana daya daga cikin kasashen aewacin nahiyar Afirka da ake baiwa makarantun kur’ani mai tsarki matukar muhimmanci, kasanrtuwar akasarin mutanen kasar mabiya addinin musulunci ne da suke kula da lamrin kur’ani, kamar yadda kuma ake ganin zai taimaka matuka musamman ga masu son bin shirin ta hanyar radio.
1446984

Abubuwan Da Ya Shafa: aljeriya
captcha