IQNA

Koyarwar Kur’ani Mai Tsarki Na Gina Mutum Domin kai Wa Matsayinsa

20:33 - September 10, 2014
Lambar Labari: 1448989
Bangaren kasa da kasa, koyarwar kur’ani mai tsarki tana kai mutum zuwa ga hakikanin matsayinsa da Allah ya yi masa na mafi daukakar halittu baki daya wanda kuma ta hakan ne zai iya kaiwa ga samun yardarm ubangijinsa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, daya daga cikin daliban jami’ar Almostafa ta duniya Sadiq Hussain wanda ya kamala karatu a bangaren kur’ani kuma a darar karatu ta digiri na uku ya bayyana cewa, hakika koyarwar kur’ani mai tsarki tana kai mutum zuwa ga hakikanin matsayinsa da Allah ya yi masa na mafi daukakar halittu baki daya wanda kuma ta hakan ne zai iya kaiwa ga samun yardar Allah madaukakin sarki.
Dalibin ya gabatar da bayani ne a lokacin da yake rubutun da ya yi a bangaren da ya yi karatu a kansa, kuma hakan ya samu karbuwa daga malaman da suka sautrare shi, musamman ma bayan da ya karba tambayoyin da aka yi masa kan hakan.
Sadiq ya bayyana cewa a kowane lokacin musulmi da wand aba musulmi ban a bukatar sanin kur’ani, duk kuwa da cewa shi musulmi ya yi Imani da shi da abin da ke cikinsa, amma kowane lokaci yana da bukatuwa zuwa ga ilminsa domin samun Karin shiriya irin ta addinin muslunci wadda Allah madaukakin sarki yake shiryar da dan adam ta hanyar koyarwar manzo wanda shi ne ke aikata kur’ani da kuma koyar da shi, yayin da wand aba musulmi bas hi ma yana bukatar saninsa domin kuwa zai amfana da abn da bai sani ba.
1447893

Abubuwan Da Ya Shafa: koran
captcha