IQNA

Malaman Musulmi Da Kiristoci A Guinea Sun Mike Da Rokon Ubangiji Kan Ebola

22:17 - September 13, 2014
Lambar Labari: 1449611
Bangaren kasa da kasa, malaman mabiya addinai na muslunci da kiristaci a kasar Guinea Konacry sun mike da addu'a domin neman ubangiji ya kawo musu sauki balain nan na cutar Ebola da ta addabi kasarsu.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an Amisriyun cewa, a cikin 'yan kwanakin nan malaman addinan muslunci da kiristaci a kasar Guinea Konacry sun mike da addu'a domin neman ubangiji ya kawo musu sauki balain nan na cutar Ebola da take ta lakume rayukan mutane.

A ci gaba da bin kadun matsalar bullar kwayoyin cutar ta Ebola da kuma irin barnar hakan ya yi a cikin 'yan watanni, hukumar lafiya ta duniya ta fitar da rahoton da ke cewa cutar tana yaduwa cikin sauri, inda ya zuwa yanzu ta lakume rayukan mutane fiye da dubu biyu a cikin kasashe hutu da ta bayyana, haka nan kuma rahoton ya ce mai yiwuwa adadin wadanda za su kamu da cutar ya kai dubu ashirin kafin a iya shawo kanta.
Rahoton na hukumar lafiya da aka fitar a ranar Talata da ta gabata ya nuna cewa kimanin mutane dubu hudu ne suka kamu da kwayoyin cutar, yayin da mutane fiye da dubu biyu daga cikinsu suka riga mu gidan gaskiya, ko a ranar Alhamis da ta gabata ma hukumomin kiwon lafiya a Najeriya sun ce wani likita ya rasa ransa a birnin Patakwal na jahar Rivers sakamakon kamuwa da kwayoyin cutar, wanda hakan ya cika adadin wadanda suka rasa rayukansu a Najeriya sakamakon kamuwa da cutar zuwa mutane 6, yayin da a kasar Senegal ma mahukuntan kasar suka sanar da cewa cutar ta Ebola ta bulla a cikin kasar, bayan da wani mutum dan kasar da yake zaune a kasar Guinea ya dawo gida, an kuma tabbatar da cewa yana dauke da kwayoyin cutar.
Wannan cuta ta Ebola wadda aka gano ta tun a cikin sheakarun da suka gabata a kasar Congo ta fara yaduwa a ne a kasar a cikin shekara ta dubu da dari tara da casein da biyar inda aka fi sanin daddobi musamman birai su ne suka fi kamuwa da cutar fiye da bil adama, a farko shekara ta dubu biyu da hudu kwatsam sai ga wannan cuta ta bulla a kasar Guinea Conakry da wani yanayi mai matukar muni da kan kashe dan adam cikin kankanin lokaci, kafin daga bisani kwayoyin cutar su bayyana a wasu kasashen na yammacin nahiyar Afirka.
Yanzu haka dai wasu rahotanni da mujallar nature ta buga na nuna cewa an gudanar da gwajin maganin cutar kan wasu birai da suke dauke da kwayoyin cutar, kuma gwajin ya gudana a cikin nasara. Yanzu haka dai an zura ido domin ganin irin sakamakon wannan yunkuri na dakile wannan mummunar annoba ta Ebola, musamman ma  akasashen da kwayoyin cutar suka bulla a yammacin nahiyar Afirka.
1449300

Abubuwan Da Ya Shafa: guinea
captcha