IQNA

Turkiya Ta Gayyaci Malaman Addinin Musulunci Na Litin Amurka Zuwa

19:30 - September 17, 2014
Lambar Labari: 1451246
Bangaren kasa da kasa, kasar Turkiya ta gayyaci malaman addinin muslunci daga yankin Latin Amurka zuwa wani taro na malaman addini daga kasashen duniya domin tattauna batutwa da suka shafi al'ummar musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, cibiyar malaman muslunci a Turkiya ta gayyaci malaman addinin muslunci daga yankin Latin Amurka zuwa wani taro na malaman addini daga kasashen duniya domin tattauna batutwa da suka shafi al'ummar musulmi da kuma fito da hakikanin surar musulunci a ido duniya.

Bayanin ya ce shugaban cibiyar malaman addinin muslunci a kasar Turkiya Muhimman Kurmez ne ya bayyana hakan a ziyarar da yake gudanarwa a kasashen latin Amurka, inda yake ganawa da al'ummomin musulmi da suka hada da malamai da kuma dalibai gami dam asana daga cikinsu da ke taka rawa a bangarori daban-daban na addinin.

Ya ce za a gudanar da taron a kasar Turkiya tare da halartar malamai daga kasashen nahiyar Asia, nahiyar Turai, nahiyar Afirka, inda dkkanin wadanda za su halarci taron za su bayyana mahangarsu kan yadda za a kara fadada ayyukan wayar da kan al'ummomin duniya dangane da yadda suke kallon addinin muslunci, musamman ma a wanann zamani inda wasu kallon addinin muslunci da mahanga maras kyau.

1450558

Abubuwan Da Ya Shafa: turkey
captcha