IQNA

Wasu ‘Yan Wasan Kallon Kafa Na Kasar Kamaru Sun Musulunta

10:13 - September 19, 2014
Lambar Labari: 1451366
Bangaren kasa da kasa, wasu matasa da ke wasan kwallon kafa a kasar Kamaru sun karbi a dddinin muslunci a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, gungun wasu matasa da ke wasan kwallon kafa a kasar Kamaru sun samu shiriya ta hanayar karbi a dddinin muslunci a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa, bayan fahimtar cewa shi ne addini na gaskiya.
Babban jami’I mai kula da harkokin addini a birnin Dubai Jawid Khatib ya bayyana cewa, dukkanin matasan suna wasan kwallon kafa ne a kungiya guda, kuma dukkanin su 23 ne suka karbi addinin muslunci tare da masu horar da su, bayan sun kwashe kimanin watanni biyu suna samun wani horo na kwallon kafa a kasar, kuma sun yi hakan ne  akan kashin kansu ba tare da wani ya ja hankalinsu ba.
Ya kara da cewa wannan kungiyar kwallon kafa ta kunshi matasa ne marassa galihu da marayu a kasar ta Kamaru, kuma sun karbi muslunci ne a lokacin da suke bin addinin kiristanci tare da bayyana cewa sun fahimci cewa a cikin addinin muslunci ne ake aiwatar da abin da addinin kiristanci na hakika ya zo da shi, domin kuwa a bubuwa da suke ci da wadanda suke sha da aka haramta  addininsu a musulunci ma haka lamarin yake, amma a addinin muslunci ne ake yin haka a aikace, saboda haka shi ne addinin gaskiya mai aikata umarnin Allah.
A kowace shekara ana samun mutanen da suke karbar addinin muslunci a kasar hadaddiyar daular larabawa da suke zuwa domin yawon shakatawa.
1450901

Abubuwan Da Ya Shafa: kamaru
captcha