IQNA

Kur'ani Magani Ne Ga Matsaloli Da Addabar Ruhin Dan Adam

23:21 - September 21, 2014
Lambar Labari: 1452344
Bangaren kasa da kasa, kurani mai tsarki yanamatsayin magani ne ga matsaloli da suke addabar ruhin dan adam ba gangar jiki ba domin kuwa shi ne magani mai warkar da cututtuka na zuciya.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo cewa, daya daga cikin mabobin kwamitin bincike na jami'ar Azahar Muhammad Shuhat Al-jundi ya bayyana cewa kurani mai tsarki yanamatsayin magani ne ga matsaloli da suke addabar ruhin dan adam, sabanin abin da wasu ke fada domin kuwa shi ne magani mai warkar da cututtuka na zuciya ma'ana ruhin bil adama.

Malamin ya ci gaba da bayani da cewa da dama sun tafi a kan tunanin cewa kur'ani magani ne na gangar jiki bisa wasu dalilai nasu, amma abin da ya bayyana a fili shi ne tasirinsa yana tattare da ruhin ne, domin kuwa Allah madaukakin sarki ya sanya kur'ani mai tsarki ya zama shiriya gag a dan adama lokacin da ya yi aiki da abin da ke cikinsa, bayan haka kuma jin abin da ke cikinsa na ayoyi masu tsarki suna da tasirinsu na musamman a kan ruhi, wanda sakamakon hakan ruhi kan natsu har ma ya samu waraka daga cututtuka da suke addabarsa.

Ya kara da cewa akwai wurare wadanda an yi bayani kan magani na gangar jiki ta hanyar yin amfani da wasu abubuwa, kamar misalign zummuwa wadda aka bayyana ta cewa tana amfanoni masu tarin yawa ga mutum da ma wasu abubuwa wadanda masana harkokin magunguna suna amfana da su daga kur'ani mai tsarki.

1451607

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha