IQNA

Radio Kur’a Na Kasar Masar Shi Ne Yawan Masu saurare A Cikin Ramadan

22:38 - September 25, 2014
Lambar Labari: 1453952
Bangaren kasa da kasa, wani bincike da aka gudanar dangane sauraren shirin radio a kasar Masar baki daya a cikin Ramadan da ya gabata ya nuna cewa gidan radio kur’ani ya fi kowane gidan radio yawan masu saurare.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Albawaba News cewa, babban sakataren hukumar kula da gidajen radio na kasar Abdulkhaliq Yusuf ya bayyana cewa, bias jin ra’ayi da suka gudanar dangane sauraren shirin radio a kasar Masar baki daya a cikin Ramadan da ya gabata ya nuna cewa gidan radio kur’ani ya fi kowane gidan radio yawan masu saurare a fadin kasar baki daya.
Ya ci gaba da cewa shi ya kasance daya daga cikin wadan sukka shirya wannan jin ra’ayi na jama’a da kuma bincike kan sauraren radio a kasar Masar a cikin watan Ramadan da ya gabata, kuma sakamakon da suka samu ya tabbatar da cewa al’ummar kasar suna sauraren karatun kur’ani a cikin watan a shirin radio fiye da sauraren kowane irin shiri.
Kasar Masar dai ta kasance kan gaba wajen gudanar da shirye-shirye na kur’ani mai tsarki fiye da kowace kasa a cikin kasashen larabawa, wannan ne ya sanya kasar ta zama  akanga a tsakanin dukaknin kasashen musulmi wajen yawan makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki a tsawon tarihinta, inda har yanzu ake buga misali da ita ta wannan bangare, kasantuwar manyan makarantan kur’ani na wannan karni duk suna a kasar Masar ne, kuma da dama daga cikinsu sun riga gidan gaskiya, amma har yanzu ana bin salonsu na karatu.
1453404

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha