IQNA

Malamn Musulmi A Duniya Sun Yi Allah Wadai Da 'Yan Ta'addan Daesh

16:59 - September 27, 2014
Lambar Labari: 1454566
Bangaren kasa da kasa, a wata wasika ta manyan malaman addinin muslunci mabiya mazhabobi daban daban a duniya sun yi kakkausar da yin Allah wadai da ayyukan kungiyar 'yan ta'adda ta daesh a kasashen Syria da Iraki da ma sauran kasashen musulmin yankin.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo Islam Online cewa, a jiya malaman addinin muslunci mabiya mazhabobi daban daban a duniya a cikin wata wasika da suka sanya ma hannu sun yi kakkausar da yin Allah wadai da ayyukan kungiyar 'yan ta'adda ta daesh a kasashen muuslmi.

Wasu rahotanni sun ce yan ta'addan ISIS sun rusa wani babban masallaci mai tsawon tarihi da ake kira masallacin Arba'in da ke cikin garin Tikrit a lardin Salahuddin da ke arewacin kasar Iraki.  
Kamfanin dillancin labaran Saumariyyah News ya bayar da rahoton cewa, 'yan ta'addan sun tarwatsa masallacin ne baki daya a yau bayan da suka dasa wasu nakiyoyin a cikinsa, kuma suka yi amfani da na'urorin tayar da bama-bamai daga nesa wajen rusa shi, masallacin dai ya kasance daya daga cikin masallatai mafi dadewa a kasar Iraki da aka gina shi tun lokacin tabi'ai.
'Yan ta'addan ISIS dai sun rusa masallatai da wuraren ibada da dama  a cikin kasashen Iraki da Syria, da hakan ya hada har da kabrukan annabawa da na sahabbai da sauran bayin Allah, lamarin da malaman addinin muslunci a kasashen daban-daban da suka hada hard a na babbar jami'ar muslunci ta Azahar da ke Masar suka bayyana hakan da cewa ba addinin muslunci ba ne.
1454006

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha