IQNA

An Yi Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da 'yan ta'addan ISIS A Faransa

23:14 - September 28, 2014
Lambar Labari: 1455029
Bangaren kasa da kasa, mata da dama sun gudanar ad jerin gwano a cikin biranan kasar faransa domin Allah wadai da 'yan ta'addan ISIS da kuma irin ayyukan ta'addanci da suke iakatawa kan al'ummar musulmi da sauran al'ummomi na Iraki da siriya a cikin lokutanan

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo cewa, mata da dama ne suka gudanar da jerin gwano domin yin Allah wadai da 'yan ta'addan ISIS da kuma irin ayyukan ta'addanci da suke iakatawa kan al'ummar musulmi da sauran al'ummomi na wasu kasashen da ma ban a musulmi ba.

A wani rahoton kuma kasar Faransa ta ce ba tada  da niyyar tattaunawa da ‘yan ta’adan da sukayi  garkuwa da wani dan kasar a yankin tinzu u na kasar algeri, shugaba kasar ne ya bayana hakan locacinda yake bayani ga manema labarai a birnin na kasar Amurka, inda ya jadada cewa gwamnatin kasarsa ba zata tattaunawa ba da ‘yan ta’ada, ko kuma yin biyaya ga barazanar su, aman zata matsa kaimi domin ganin ta kubutarda da kasar ta.

A daren lahadi nan ne wasu ‘yan bindiga suka yi awan gaba da bafaranshe dan yawon bude ido mai suna gourdel dan shekaru hamsin da biyar a garin tizi  dake da nisan kilometa dari da babban birni alger.

Tunda fari dai kasar Faransa ta yi gargadi zuwa yan kasar dake kasashen waje da su yi taka sasan bayan da kungiyar ISIS ta sanar da cewa zata kadamar da yaki da Faransawa dama Amarukawa a sassa daban daban na Duniya nan saboda yakin da suka shelanta kan ‘yan kungiyar ta ISIS.

1454263

Abubuwan Da Ya Shafa: faransa
captcha