Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almujaz cewa, a yau kwamitin da ke kula da fitar da fatawoyi na cibiyar addinin muslunci ta kasar Masar wato Azahar ya fitar da wani bayani da ke nuna rashin amincewa da nuna fusakun annabawan Allah a cikin fina-finan da ake nunawa a gidajen sinima a kasar da ma wajenta.
Bayanin ay ci gaba da bisa la'akari da wasu dalilai na shari'a da kuma matsayn annabawa ubangiji, bai ya halasta a shar'ance a nuna fuskar wani annabi daga cikin annabawan Allah a fim, domin hakan yana matsayin rage matsayinsa ta hanyar bayyana fuskarsa da wani mutum na daban kamar dai yadda kwamitin ya sanar a cikin bayanin nasa.
Al'ummar kasar Masar suna bayar muhimamnci matuka ga fina-finai da ake fitarwa domin nuna su a gidajen sinima, haka nan kuma suna kallon wadanda ake nunawa a gidajen talabijin da ake ci gaba das u lokaci zuwa lokaci, kuma akwai mutanen da suke shirya irin wadannan fina-finai an san su a kasar.
Kafin wanann lokacin da ministan al'adu na kasar Masar Jabir Usfur ya bayyana cewa bayyana fusakun annabawa bai sabawa shari'a ko kaidoji na addinin muslunci ba.