Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa shugabar kula da ayyukan kwamitin Zahra Naghiy Zadeh ta bayyana cewa, nan da watan goma na shekarar shamsiya ne za a gudanar da gasar karatun kur'ani da kuma harda ta daliban jami'a da ake gudanarwa a matsayi na kasa da kasa abirnin Tehran, fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu an riga an fara gudanar da dukaknin shirye-shiryen da suka kamata domin tabbatar da cewa an gudanar da wanann gasa alokacin da aka ayyana, wanda kuma shi ne karo na biyar da za a gudanar da ita tare da halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya da suka hada da na larabawa da kuma na musulmi.
Yanzu haka dai akwai nauoin gasar kur'ani da ake shiryawa a jamhuriyar muslunci ta Iran da nufin karffa ayyukan kur'ani a tsakanin al'ummar musulmi, inda akan shirya gasa ta kasa da kasa wadda take hada makaranta da mahardata daga koina cikin fadin duniya, yayin da kuma ke shirya irin wannan gasa wadda ta kbanci daliban jami'a kawai musulmi daga koina cikin fadin duniya, wanda kuma jamhuriyar musulunci ta Iran c eta fara aiwatar da wanann shiri a tarihn gasar kur'ani.
1457403