IQNA

An fara Wani Shiri Na Horar Da Malaman Kur’ani 100 A Iraki

23:14 - October 07, 2014
Lambar Labari: 1458052
Bangaren kasa da kasa, an fara aiwatar da wani shiri a haramin Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf mai alfarma na horar da malaman kur’ani mai tsarki su 100 a cikin wannan hubbare.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga bangaren yada labaran birnin Alawi cewa an riga an fara aiwatar da wani shiri a haramin Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf mai alfarma na horar da malaman kur’ani mai tsarki su 100 a cikin wannan hubbare mai albarka a cikin wannan mako.
Bayanin ya ci gaba da cewa an shirya wannan horo ne da nufin karfafa ayyukan kur’ani mai tsarkia  kasar, kasantuwar al’ummar kasar na da matukar bukatuwa zuwa wadanda za su tsaya wajen koyar da yara kanan a makarantu tare da makarantun gaba da firamare akasra ta fiskar kur’ani mai tsarki, wanda kuma yin hakan zai bayar da damar yaye malamai 100 wadanda su kuma za su yaye daruruwa.
Kasar Iraki na daga cikin kasashen musulmi da aka haramta wa amfana da hasken kur’ani a makarantui a lokacin mulkin danniya da kama karya karkashin tasirin kasashen yammacin turai, wanda kuma tun bayan kawo karshen mulkin firaunanci a kasar, al’umma ta rungumi kur’ani da koyarwarsa tare da mayar da hanakalin wajen ganin yara masu tasowa sun amfana da koyarwara domin rayuwarsu ta gaba.
1457851

Abubuwan Da Ya Shafa: Iraq
captcha