IQNA

Amurka Ba Ta Kai hare-Hare kan sansanonin 'yan Ta'addan ISIS

20:32 - October 10, 2014
Lambar Labari: 1458733
Bangaren kasa da kasa, jiragen yakin Amurka da ke kai hari basu nugfar sansanonin 'yan ta'addan ISIS a cikin yankunan kasar Iraki illa dai kawai ana wasa da hankulan al'ummimin duniya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar Al-alam cewa, wani daya daga cikin na hannun damar Muktada sadr ya bayyana cewa jiragen yakin Amurka da ke kai hari basu nugfar sansanonin 'yan ta'addan ISIS a cikin yankunan kasar Iraki sai dai kawai ana farfaganda hakan ne kawai domin ccimma manufa ta siyasa.

Wani rahoton majalisar dinkin duniya da aka fitar a yau Alhamis ya yi nuni da cewa, 'yan ta'addan ISIS da ke da'awar jihadi a Iraki da Syria, sun kashe fararen hula dubuta tara da dari uku da arba'in da bakawai a cikin wannan shekara ta dubu biyu da goma sha hudu a kasar Iraki.
Rahoton wanda manzon musamman na majalisar dinkin duniya ya harhada tare da sauran ma'aikatan da ke aiki a karkashinsa, ya tababtar da cewa 'yan ta'addan na ISIS suna kisan na dabbanci a kan fararen hula ba ji ba gani a cikin yankunan da ke arewacin Iraki, haka nan kma sun sace dubban matan aure da kuma 'yan mata wadanda suke yin amfani da su ta hanyar yi musu fyade, haka nan kuma suna tilasta kananan yara daukar makami tare da tilasta su aikata laifukan kisan kai.
Rahoton ya ce fiye da rabin mutane dubuta tara da dari uku da arba'in da bakawai da 'yan ta'addan ISIS suka kashe  a Iraki a cikin wanann shekara, sun kashe su ne daga watan Yunin da ya gabata zuwa karshen watan Satumban da ya gabata, yayin da kuma suka tilasta fararen hula fiye da miliyan daya da digo takwas barin gidajensu tare da mayar da su 'yan gudun hijira.
1458669

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha