IQNA

Mutane Miliyan 2 Ne Ke Ziyartar Kabarin Amirul Muminin (AS) Da Furanni 30,000 Na Iran

23:24 - October 12, 2014
Lambar Labari: 1459704
Bangaren kasa da kasa, a ci gaba da isa birnin najaf mai tsarki da mabiya ahlul bait ke yi domin ziyarta Amirul muminin (AS) a hubbarensa dake birnin mai tsarki fiye da mutane miliyan biyu suke ziyara a wurin.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bilad News cewa jama a na ci gaba da isa birnin najaf mai tsarki da mabiya ahlul bait (AS)ke yi domin ziyartar Amirul muminin Ali dan Abu Talib(AS) a hubbarensa da ke can.

A nasa bangaren shugaban jamhuriyar muslunci ya bayana cewar jamhuriya musulinci zata yi duk abunda ya dace domin kare wurare masu tsarki na musulmai a kasar Iraki. shugaban  wanda ke bayana hakan yayin da 'yan ta'ada a kasar ta Iraki ke korarin sun rusa kasar da kuma kwace mulki ga gwamnatin kasar, yace jamhuriyar Islama a shirye take ta dafa ta kowane hali domin kare yuraren ibada na musulmai.  

Ya kara da cewa un kafin wannan lokaci sun gargadi Amurka da sauran kasashen da suke mara baya ga ayyukan ta'addanci a yanki das u san cewa abin da suke yi zai dawo daga bisani ya gagare su, kuma wannan shi ne abin da yake faruwa, domin kuwa 'yan ta'addan da suka kafa sun dawo sun gagare su har ma suna yi musu barazana.

Wannan ziyara da ake gudanarwa a Najaf a ranar Gadir na daga cikin ayyukan raya sh'air na ubangiji da mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah suke yi.

1459047

Abubuwan Da Ya Shafa: najaf
captcha