IQNA

Taron Kusanto Da Mazhabobin Muslunci A Birnin Karbala Mai Alfarma

21:57 - October 13, 2014
Lambar Labari: 1459789
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taro na kusanto da mahangar mazhabobin addinin muslunci a birnin karbala mai alfarma na kasar Iraki da nufin kara samun daidaito da kuma fahimtar juna a tsakanin mabiya addinin muslunci.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alkafil cewa  jiya an gudanar da wani taro na kusanto da mahangar mazhabobin addinin muslunci a birnin karbala mai alfarma na kasar Iraki da nufin kara samun fahimtar juna a tsakanin mabiya addinin muslunci mabiya mazhabobi daban-daban.

Bayanin ya ci gaba da cewa taron yana daya daga cikin irinsa da ka fara gudanarwa a birnin wanda daya ne daga cikin birane masu alfarma a cikin addinin muslunci bias la’akari da tarihinsa da kuma hubbaren iyalan gidan manzon Allah da sahabbnsu da ke wurin, wanda hakan ya sanya ake bayar da muhimamnci wajen gudanar da tarukan addini a cikinsa musamman a babban dakin taruka na hubbaren Imam Hussai tsira da amincin Allah su tabbata  agare shi.

Babbar manufar taron dai ita ce kokari na dunke irin barakar da makiya addinin muslunci suke kokarin haifarwa tsakanin muaulmi da sunan banbanci mazhaba ko fahimta, wanda kuma ake yi amfani da wasu malamai da suka sayar da lahirarsu domin cimma wannan manufa ta makiya addini, da dama daga cikin malamai da suka gabatar da jawabaoi sun jaddada wajabcin zama cikin fadaka dangane da makircin da ake kullawa musulmi da musulunci.

1459592

Abubuwan Da Ya Shafa: karbala
captcha