Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, mahukuntan kasar Saudiyya sun yanke hukunci kisa kan Ayatollah Namir Baqir namir sakamakon sukar salon mulkin mulukiya na gidan sarautar Al-saud a kasar.
An gudanar da zanga-zangar lumana a kasar yankunan awamiyya da Katif da ke gabacin kasar Saudiyya, da ke neman a saki fursunonin siyasa da mahukuntan kasar ke tsare da su. Masu zanga-zangar sun fit one duk kuwa barazanar da mahukuntan kasar saudiyya suka yi kan shiga kafar wando daya da duk wanda ya gudanar da wata zanga-zanga ko gangami da ke kalu balantar mahukuntan kasar.
Dubban jami'an tsaro ne a cikin kayan sarki suka isa yankunan daban-daban da ke gabacin Saudiyya, domin hana gudanar da irin wannan zanga-zanga, amma duk da hakan al'ummomin yankunan Al-awamiyya da Katif sun fito kan tituna, dauke da hotunan daruruwan mutanen da gwamnatin saudiyya take tsare da su tsawon shekaru saboda dalilai na siyasa, ba tare da gurfanar da su gaban kuliya ba.
A wani mataki na yunkurin kaucewa boren al'umma kamar yadda ya faru a wasu kasashen kuma yake ci gaba da faruwa a kasashen larabawa da dama, mahukuntan kasar Saudiyya sun sha alwashin kyautata rayuwar talakawa, tare da kara samar da guraben ayyuka ga masu zaman kashe wando a kasar.
1460515