IQNA

An Fara Gudanar da Gasar Hardar Kur'ani Mai Tsarki Da Tajwid A Kasar Oman

22:59 - October 20, 2014
Lambar Labari: 1462263
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki tashekara a kasar Oman tare da halartar makaranta da mahardata daga sassa na kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Oman Daily cewa, babban jami'I mai kula da ayyukan kur'ani na kasar Said Hamid Adawaini ya bayyana cewa, a cikin wannan makon ne aka fara gudanar da share fage na gasar karatun kur'ani mai tsarki tashekara a kasar Oman tare da halartar makaranta da mahardata daga sassa na kasar kamar dai yadda aka saba.



Ya ci gaba da cewa a wanann karon gasar ta dauki sabon salo, domin kuwa ba a takaita tad a bangarori na kir'a da kuma harda ba kawai, an kara hard a bangaren tajwidi wanda idan mahalaertan suna bukata za su iya yin rijistar sunayensu a duk bangaren da suke son su gudanar da gasa a cikinsa.



Kasar Oman dai na daga cikin kasashen larabawan yankin gabas ta tsakiya da ke bayar himma matuka wajen habbaka ayyuka da suka danganci kur'ani mai tsarki, da hakan ya hada da shirya gasa wafa kan hada dukaknin bangarori na makaranta da mahardat na kasar baki domin su hadu wuri guda su gudanar da gasa, wanda hakan yana da bababn tasiri wajen habbaka lamurran ku'ani a tsakanin al'ummar kasar wadanda akasarinsu mabiya addinin muslunci ne.



1461486

Abubuwan Da Ya Shafa: oman
captcha