IQNA

An Rarraba Kur'anai A Asibitocin Kasar Algeria Ga Marassa Lafiya

23:23 - October 26, 2014
Lambar Labari: 1464221
Bangaren kasa da kasa, an fara aiwatar da wani shiri na rarraba kwafin kur'ani mai tsarki a wasu daga cisibitocin kasar Aljeriya ga marssa lafiya da nufin samun waraka.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Alkhabar ta kasar Aljeriya cewa, a cikin wannan mako an fara aiwatar da wani shiri na rarraba kwafin kur'ani mai tsarki a wasu daga cisibitocin kasar Aljeriya ga marssa lafiya da nufin samun waraka kamar dai yadda ruwayoyi da daman a addini suka tabbatar da cewa shi kr'ani waraka ne ga abin da ke cikin kiraza.

Wadannan kwafi-kwafi na kur'ani dai hukumar kula da ayyukan addini bangaren kur'ani c eta dauki nauyin rarraba su ga marassa lafiya, wanda kuma an fi mayar da hankali wajen raba su ga mutane da suke da damar da za su iya karantawa domin samun sauki daga ciwonsu, kamar yadda kuma akwai shiri na sauraren karatunsa.

An gudanar da bincike dangane da wannan batu a manyan cibiyoyin bincike na kasashen turai da ma wasu kasashen duniya na daban, inda aka gane cewa sauraren karatun kur'ani mai tsarki yana kawo sauki matuka ga wasu ciwuka, tare da sanya natsuwar zuciya ga mai saurarensa.

1463338

Abubuwan Da Ya Shafa: algeria
captcha