Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Global News cewa wasu daga cikin mutanen kasar Canada daga birnin Cold Lake wadanda ba musulmi suna nuna cikakken goyon bayansu ga musulmi da ake nuna musu karan tsana da cin mutuncinsu a kasar a cikin lokutan nan.
Mutanen dai sun dauki wannan mataki ne bayan da wani dan kasar mai tsananin gaba da muslunci ya yi rubutun batunci a kan wani masallaci na musulmi, kamar yadda ya yi hakan a wani wurin shakatawa inda ya bakanta sunan muslunci tare aibanta shi ga sauran mutane wadanda ba musulmi ba.
Rahoton ya ci gaba da cewa irin wannan lamari ya sha faruwa akasar ta Canada duk kuwa da cewa babu wani mataki na azo a gani da gwamnatin kasar atke dauka domin shiga kafar wando daya da masu cin zarafin muslumi da addinin muslunci a kasar, kasantuwar mahukuntan kasar da ke mulki suna goyon bayan siyasar gaba da muslulmi ido rufe irin ta haramtacciyar kasar yahudawa.
1463807