Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa cewa jami’an tsaron Sudiyya sun sanar da kamo mutanen da su ka kai harin ta’addanci akan ‘yan shiyar da ke juyayin Ashura a wani kauye da ke gabacin kasar.
Tashar telbijin din arabiyya ta Saudiyya ta ambato majiyar tsaron kasar na cewa; an kame mutane tara wadanda su ka kai harin a yankin Ihsaa da ke gabacin Saudiyya a daren jiya wanda ya yi sanadin shahadar mutane 7 da jikkata wasu, mafi yawancinsu kananan yara. Bugu da kari majiyar ta ce; mutanen sun shirya kai wasu hare-haren a cikin garuruwan Khubar da Qatif da ke gabacin kasar inda mafi yawancin mutanensa ‘yan shi’a ne.
Harin na jiya ya zo ne dai a lokacin da ake rayuwa cikin zullumi a gabacin Saudiyya din, bayan yanke hukumcin kasa da wata kotun kasar ta yi wa daya daga cikin fitattun malaman shi’ar kasar Sheih Nimr.