Ko shakka babu da akwai dalilai masu yawa da su ka taka rawa wajen ci gaba da kuma wanzuwar Ashura.. Dalili na farko dai shi ne nufin Allah, kamar yadda ya ke fada a cikin aya ta 8 suratu “Saf” “Suna son su dushe hasken Allah, amma Allah mai cika haskensa ne.” Kasantuwar yunkurin Imam Husain (a.s) na Ashura, mai nufin kare addinin musulunci ya shiga karkashin wannan fadar ta Ubangiji.
Saboda haka baya ga kiyaye wannan hasken da Ubangii madaukakin sarki ya yi, kuma aduk lokacin da zamani ya ke kara ja, yana kara karasashi. Ya zo a cikin nassi na hadisi cewa; " Shahadar Imam Husai tana da karasashi a cikin zukatan mutanen wanda ba zai taba dushewa ba." Bugu da kari, wani daga cikin dalilan wanzuwar Ashura' shi ne yadda manzon Allah (s.a.wa.) ya yi maganganu akan matsayin Imam Husain (a.s).
A tsawon tarihin musulunci kuwa al'ummar musulmi sun zama masu girmama da ganin matsayin maganganun manzon Allah (s.a.wa.). Adailin haka ne malaman addinin musulunci da dukkanin mazhabobinsu na sunna da shi'a su ke wajabta yin biyayya ga manzon Allah (s.a.w.a). A cikin suratu Nisa'i, aya ta 80 Allah madaukakin sarki ya bayyana wajabcin yin biyayya ga manzon Allah (s.a.w.a). Kuma a cikin ayoyin na 3 da 4 na suratu Najm, Allah madaukakin sarki ya bayyana cewa duk abinda manzon Allah (s.a.w.a) ya fada ya samo tushe ne daga wahayi. Manzon Allah (s.a.w.a) ya yi magana akan matsayin Imam Husain (a.s) da bayyana shi a cikin wani hadisinsa da cewa; shi jagorane.
Daya daga cikin sahabban manzon Allah (s.a.wa) ya nakalto daga manzon Allah (s.a.wa.) cewa; "Kai jagora ne, kai dan jagora ne kuma mahaifin jagorori. Kai imami ne kuma dan imami da mahaifin imamami. Kai hujja ne kuma dan hujja kuma mahaifin hujjoji. Mahaifin jagorori tara ne kuma na taransu shi ne ma'abocin tsayuwa."
Baya ga ambaton matsayar Imam Husain (a.s.) da manzon Allah ya yi, ya kuma yi hasashen yin shahadarsa. Fitaccen masanin hadisan nan na ahlusunnah Athir al-Razy, ya nakalto daga Ash'as Bin Sahaim daga mahaifinsa daga manzon Allah (s.a.wa) yana cewa: " Dana, Husain (a.s) zai yi shahada a wani wuri a kusa da Iraki, duk wanda ya riske shi wajibi ne ya taimaka masa." Wani hadisin daga A'isha matar manzon Allah (s.a.w.a) ta rawaito cewa manzon Allah ya sumbaci Husain (a.s) sannan ya ce; "Duk wanda ya ziyarci kabarinsa yana da lada na aikin haji."
Irin tarukan da ake gudanarwa a wadannan lokuta na Ashura na nuni da irin karbuwar da wannan munasaba ta samua tsakanin muslumi da suka hada das u kansu mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) da kuma sauran musulmi, wadanda suke gane matsayin wannan gida mai albarka da iyaansa da kuma zaluncin da aka yi musu.