IQNA

Khalid Mash’al Ya Kirayi Palastinawa Zuwa Ga Wani Sabon Bore Kan Isra’ila

18:29 - November 06, 2014
Lambar Labari: 1470577
Bangaren kasa da kasa, shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas Khalid Mashal shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas ya kirayi palastinawa adukkanin bangarori da su mike domin tayar da wani sabon bore kan haramtacciyar kasar Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na Ma’a cewa Khalid Mashal ya kirayi palastinawa  adukkanin bangarori da su mike domin tayar da wani sabon bore kan haramtacciyar kasar Isra’ila dangane da ta’addancin da take aikatawa.

Rahotanni daga kasar Palastinu da aka mamaye na nuni da cewa wani dan sandan kan iyakan HKI ya halaka kana wasu sahyoniyawan kuma kimanin 16 ciki kuwa har da 'yan sandan sun sami raunuka sakamakon wasu hare-haren daukar fansa da wasu direbobi Palastinawa guda biyu suka kai musu a birnin Qudus da kuma Yammacin kogin Jordan a jiya Laraba.
A wata sanarwa da 'yan sandan HKI suka fitar sun ce lamarin ya faro ne lokacin da wani direba Bapalastine ya kutsa da motarsa cikin taron 'yan sandan HKI inda nan take ya hallaka dan sanda guda da kuma raunana wasu. Har ila yau kuma direban ya sake kutsawa kan wasu yahudawa da suke tsattsaye a bakin hanya inda a nan ma ya raunana wasu 11 kafin 'yan sandan su harbe shi.
Sanarwar 'yan sandan ta kara da cewa hari na biyun ya faru ne a yammacin kogin Jordan inda wani direban na daban ya kutsa cikin sojojin HKI inda a nan ma ya raunata wasu daga cikin su, kafin ya samu ya ranta cikin na kare.
Kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci na Hamas da Hizbullah sun jinjinawa wadannan Palastinawa da suka kai wannan harin suna masu cewa hakan wani bangare ne na gwagwarmaya sannan kuma wani bangare ne na mayar da martani ga keta hurumin Al-Aqsa da cin mutumcin Palastinawan da HKI take ci gaba da yi.
1470551

Abubuwan Da Ya Shafa: palastine
captcha