IQNA

Ana Kokarin Karfafa Mata Domin Saka Hijabin Muslunci A Aljeriya

18:52 - November 10, 2014
Lambar Labari: 1471928
Bangaren kasa da kasa, an kafa wata cibiya da zata mayar da hankali wajen wayar da kan mata da kuma karfafa su wajen yin amfani da hijabin musulunci a kasar Aljeriya maimakon yin amfani da kaya marassa kan gado.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Alsharq cewa, an kafa wannan kungiya ne domin ta mayar da hankali wajen wayar da kan mata da kuma karfafa su wajen yin amfani da sabon hijabin musulunci a kasar Aljeriya wanda aka fi sani Hijad modern maimakon yin amfani da kaya da ba su dace da su a matsayinsu na musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan sabon hijabin yanha rufe jikin mata baki daya, duk kuwa da cewa yana da nauoi daban-daban kuma baya kama da abaya wadda mata suke sakawa da ke rufe jikinsu baki daya, amma dai kuma yafi shigar da mata suke yi a kasar ta Aljeriya wadda ke nuna tsiraicinsu baki daya, kamar yadda wasu kayan ba su rufe jikinsu, wanda kuma hakan yana illa da kuma haramci a cikin addini.
Da dama daga cikin mata a kasar sun nuna gamsuwarsu da wannan sabon tufafin hijabi, kuma ana shigowa da shi ne daga kasar Turkiya a cikin farashi mai sauki, wanda shi ma ya danganta da karfn mai saye, haka nan kuma wannan kungiya tana ci gaba da yin aikinta na wayar da kan mata ta hanyoyi da dama, da suka hada da kafofin yada labarai da aka sani talabijin da jaridu da sauransu, haka nan kuma ana amfani da shafukan yanar gizo wajen isar da wannan sako ga mata, wanda kauma  acewar cibiyar hakan yana yi gagarumin tasiri.
1471794

Abubuwan Da Ya Shafa: algeria
captcha