Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Almisral yaum cewa Nicolay Miladinov manzon musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Iraki ya bayyana cewa cibiyar Azhar ta Masar za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen yaki da masu tsatsauran ra’ayi da ke aikata ta’addanci da sunan addinin muslunci.
Ya ci gaba da cewa bisa la’akari da matsayin wannan ibiya take da shi a wurin musulmi da kuma yadda take taka rawa wajen fuskantar batutuwa da dama a bangaren addini, za ta iya yin amfani da matsayinta wajen yada sahihin ilimi da tunani irin na addinin muslunci, maimakon barin ‘yan ta’adda suna yada akidarsu da ta’addanci da sunan addini.
A cikin wadannan lokuta dai masu da’awar jihadi suna aikata barna da sunan addinin musluncia kasashe daban-daban, wanda hakan ya bar mummunan tasiri a cikin kwakwalen wadanda ba musulmi ba, musamman ma daia cikin kasashen yammacin turai, inda suke kallon muslunci a matsayin addinin ta’addanci a halin yanzu.
Ya kuma yaba da irin matakan da malaman mazhabar iyalan gidan manzo ke dauka a Iraki da kuma kokarinsu na daidaita tunain musulmi baki daya kan tnani madaidaici.