Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Alwatan ta kasar saudiyya cewa, bayan bude gasar da safe a jiya makaranta daga kasashen daban-daban sun kara, da suka hada da Bahrain, Chad, Gambia, Pakistan, Libya, Moroco, Niger, kamaru, Mauritania, Philipines da kuma Algeria.
Sai kuma da yamma da aka gudanar da bangare na biyu a rana ta farko, kasashen da suka kara da juna a yammacin na jiya sun hada da Tunisia, Indonisia, Senegal, Tajikistan, Nigeria, Kamaru, Myanmar, Bahrain, Bosni da kuma Afirka ta kudu.
Gasar dai tana samun halartar makaranta da mahardata kimanin 138 daga kasashen duniya 59 kamar dai yadda masu tsara gasar suka sanar, wanda kuma shi ne karo na talatin da shida da ake gudanar da irin wannan gasa a ta kasa da kasa a Saudiyyah.
Ana gudanar da ita e a bangaren karatun kur'ani da harda a bangaren kur'ani baki daya, sai kuma bangaren izihi 15 da kuma izihi 5, wada dukkanin bangarorin ana karawa a cikinsu.