Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarata cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, a jiya kira da a dauki dukkanin matakan da suka dace domin hana yahudawan sahyuniya gina ramuka akarkashin masallacin Quds da nufin rusa wannan masallaci mai daraja.
Ita ma a nata bangaren hukumomi da kungiyoyi suna ci gaba da yin tofin Allah tsine kan matakan wuce gona da iri da tsagerun yahudawan sahayoniyya ke dauka kan Masallacin Aksa da ke birnin Qudus na Palasdinu.
Shugaban hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa ya yi Allah wadai da harin wuce gona da iri da tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida suka kai Masallacin Aksa tare da jikkata masallata masu yawa; yana mai zargin gwamnatin haramtacciyar kasar ta Isra’ila da karfafa gwiwar maharani.
Alkalin alkalan hukumar Palasdinawa ya yi Allah wadai da harin ta’addancin da tsagerun yahudawan na sahayoniyya suka kai kan Masallacin na Aksa yana mai jaddada cewa; dukkanin wajajen ibadu na Musulunci da Kiristanci da suke birnin Qudus suka karkashin kulawar Palasdinawa ne kuma hakki ne na al’ummar musulmin duniya su dauki matakan kare wajaje masu tsarki na addini.
Kungiyoyin gwagwarmayar Musulunci na Hizbullahi da ke kasar Lebanon da na Hamas a Palasdinu dukkaninsu sun fitar da bayanan yin Allah wadai da muzanta hurumin Masallacin na Aksa, inda a jiya Laraba ce gungun tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida suka kai farmaki Masallacin tare da jikkata masallata akalla ashirin.
1474439