IQNA

Kungiyar Tarayyar Turai Ta Jaddada Wajabcin Daukar Matakan Ladabtar Da Isra'ila

21:24 - November 19, 2014
Lambar Labari: 1475303
Bangaren kasa da kasa, a zaman da ministocin harkokin wajen kasashen tarayyar turai suka gudanar sun amince kan daukar matakan da suka dace domin ladabtar da Isra'ila kan ayyuanta.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a wani labari day a dauka daga shafin sadarwa na jaridar Yadiut Ahranut ta yahudawa, an bayyana cewa ministocin harkokin wajen kasashen tarayyar turai suka gudanar sun amince kan daukar matakan da suka dace domin ladabtar da Isra'ila kan ayyuanta na yin watsi da fatally da dokokin kasa da kasa.

Babbar jami’ar Diflomasiyar Turai a nata bangaren ta yi kira da a samar da kasar Falasdinu domin kawo karshan rikici a yankin Gabas ta tsakiya, wannan kwa a daidai lokacin da ake ci gaba da samun barkewa rikici a birnin Kudus.  

Ta fadi haka ne a ziyarar da ta kai a zirin Gaza inda tace bai kamata ba a zuba ido wa wadanan kasashe da ke fama da rikici ba, don haka zata tuntunbi duk kasasshen kungiyar tarrayya Turai domin kawo karshen wanan rikici.  

Sai dai a nasa banagaren Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas yace su na kan shirin tura dabtarin kudiri zuwa Majalisar Dinki Duniya, domin kawo karshan iko da Isara’ila ke yi da yankunansu da kuma wasu kadarorin su.

Yazuwa yanzu dai kasar Suedin ce kasa Turai ta farko data  amunce da kasar Falastinu bayan kasashe 134 da suka amunce da hakan a duniya. 

1474822

Abubuwan Da Ya Shafa: turai
captcha