Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, yanakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kullul Iraq cewa, a jiya an tattauna batun yadda za a gudanar da taruukan arba’in kamar yadda aka saba a kasar Iraki tsakanin shugaban majalisar koli ta musulunci a Iraki Sayyid Ammar Hakim da kuma jakadan Iran a kasar ta Iraki Hassan Danayifar a babban ofishin kungiyar da ke cikin fadar mulkin Iraki.
Wannan dai yana daga cikin irin ayuukan da jakadan kan gudanar wajen tuntubar mutanen da suke da tasiri ta fuskanci addini a kasar musamman ma malamai da kuma manyan ‘yan siyasa domin sanin yadda za a gudanar da wasu taruka na addini da suka shafi mabiya mazhabar iyalan gidan manzo, wanda akasarin mutanen da suke halartar wadannan taruka daga kasashen ketare suna zuwa ne daga Iran.
Yanzu haka dai bayan gudanar taron ashura a ‘yan kwanakin da suka gabata, a halin yanzu an fara shirye-shirye gadan-gadan domin tababtar da cewa tarukan arba’in sun gudana kamar yadda aka saba cikin kwanciyar hankali, duk kuwa da cewa dai kasar tana fuskantar manyan matsaloli da kalu bale na tsaro, sakamakon bayyanar ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi da ke kashe musulmi.
1474968