IQNA

Iran bayan juyin juya halin musulunci ta zama daga cikin manyan kasashe na duniya

Bangaren dake kula da kasa da kasa: Iran bayan juyin juya halin musulunci ta kama hanyar neman yanci,tsayin daka da kuma zama mai karfi a yankin dama duniya.
Said Ihsan Kadi Zade mai kula ofishin al'adu na jamhuriyar musulunci ta Iran a Kurwasiya a wata tattaunawa ta wayar tarho da dan jaridar bangaren hulda ta kasa da kasa a cibiyar watsa labarai na Kur'ani a Iran Iqna ya bayyana cewa: Iran bayan juyin juya halin musulunci ta fuskanci tsananin matsin lamba da takunkumin karya tattalin arziki da matakai na siyasa masu yawa iri-iri,gurbata al'adu da kallafa mata yaki da nuna mata wariya a duk wata hulda ta kasa da kasa. Hakan ya sa Iran ta kama hanyar neman yanci,tsayindaka da karfafa duk wata madoga da ci gaba ,cikin ikon Allah hakan ya zama alheri da zama mafi karfi a yankin dama duniya.
Ya kara nuni da tasirin juyin juya halin musulunci na Iran ga al'ummomi intattu masu neman yanci da cewa; Juyin musulunci na Iran ya samar da wani sabon yanayi da sauyi a duniya,wannan sauyi ya isa ga sauran kasashe musamman al'ummomin musulmi da kara masu karfi da ruhin tsayindaka da dogaro da al'umma a matsayin karfi mafi karfo.Kadi Zade ya kara da cewa: mu a yanzu tasirin juyin musulunci ya shafi dukan bangarori a yau a kasashen musulmi a nahiyoyin Asiya da Afrika kuma mun shaida da yadda al'ummomi ke kara runguma da dogaro da kai a duk wani abu day a shafi jama'a da zamantakewa.

358220