IQNA

Washigton za ta karbi bakuncin kasuwar baje kolin finafinan mususulmi ta kasa da kasa

Bangare hulda ta kasa da kasa: Kasuwar baje koli ta kasa da kasa karo na biyu kan finafinan musulunci za a gudanar daga ranar 25 ga watan Bahman har zuwa 22 ga watan Isfad na wannan shekara a birnin Washigton na Amerika.
Cibiyar koyar da Alkur'ani ta Iran Iqna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Muslimfilm ta watsa rahoton cewa: a wannan kasuwar baje koli za a kaddamar da fina-finai ne musulmi a fadin duniyar musulunci suka shirya karkashin taken kwarewa cikin tsanani kuma za a kwashe kwanaki 28 a cikin jami'o'I biyar na Amerika ana gudanarwa kuma wadannan jami'o'I sune Jorge Tawn,Jorge Washigton,Jorge Mison da Moriland duka a Washington.

Sanin hakikanin Musulmi a duniyarmu ta yau, binciken sanin bambancin al'adu da tunanin musulmi a fadin duniya,girman yafewa da fahimtar juna ta hanyar tattaunawa tsakanin musulmi da wanda ba musulmi ba na daga cikin dalilan shirya wannan kasuwar baje koli karkashin majalisar koli ta musulmin Amerika.Ita dai majalisar koli ta musulmin Amerika mai zaman kanta an kafa tan e a shekara ta 2001 inda musulmin Amerika suka kirkiro tad a nufin yafewa da fahimtar juna tsakaninsu da sauran addinai da mazhabobi daban-daban kuma cibiyarta tana Washigton da reshenta a Buston da Alkahira da kuma Basra.


359318