Bangaren siyasa:Komandan sojoji a gaban manyan jami'an sojoji ya bayyana cewa:alfano da sakon juyin musulunci a tsawon tarihi ya isa ga al'ummomin duniya kuma zai ci gaba da tada su daga barci da fadakar da su ta fuskar addini,ruhi da adalci.
Cibiyar koyar da Alkur'ani a nan Iran Iqna bayan nakaltowa daga majiyar komandan sojojin ta watsa labarin cewa:komandan sojojin Iran Janar Said Hasan FiruzAbadi a gaban manyan jami'an sojojin Iran ya bayyana cewa: juyin musulunci ya taka rawa da tasiri a tsakanin al'ummomin musulmi da ma na kasa da kasa da cewa: a tsawon shekaru talatin na nasarar juyin musulunci an raya addini da ruhi ga dukan bil adama a fadin yankuna da sassa na duniya.
Ya kara da cewa: Shekaru masu zuwa ,shekaru ne da al'ummomi za su kara ringumar adalci da gwagwarmayar fuskantar masu danniya da zalunci na duniya a tsakanin al'ummomi.Ya kuma jaddada cewa: tasiri,tsarin addinin musulunci da ma'anawiya sun kara raya juyin musulunci ta dukan bangarori day a hada ilimin siyasa,zamantakewa,halayyar dan adam da fasaha.
360270