Bangaren Siyasa: Amerika bayan rugujewar Sovietik da harin ranar 11 ga watan Stumba ta yi ta kokarin ganin ta mallaki yankin Gabas ta tsakiya daga cikin kokarinta kai wa kasar Afganistan,Iraki ,labanon da Palasdinu hari amma da taimakon Allah da albarkacin juyin musulunci yankin gabas ta tsakiya mai riko da addinin musulunci yana bin jagorancin jamhuriyar musulunci a Iran.
Janar Yadullah Jawani shugaban ofishin siyasa a rundunar kare juyin juya halin musulunci na Iran a ci gaba da tattaunawar sad a cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ya yi nuni da wasu shekaru talatin na nasarar juyin musulunci a Iran da cewa:Duk takunkumin kara tattalin arziki kan Iran a yau Iran ta shiga cikin jerin kasashe masu kokarin mallakar fasahar nukliya ta zaman lafiya da kuma cikin jerin wadanda suka jefa tauraron dan adam a cikin samaniya da sauran nasarori da Iran ta cimma fiye da yadda ake zato.Sauye-sauye a tsakanin al'umma sun samo tushe ne daga matasa dam asana Iraniya masu dogaro da kai da bada himma da cewa: wannan kyakawar niya da dogaro da kai da matasa masana a Iran suka nuna shi ne ya taimaka masu wajen yakar duk wata matsala karama da babba da karfafa masu karfin gwiwar cimma nasarar abin da suka sa gaba.A yau matsa a jamhuriyar musulunci a Iran suna dogaro da Allah da neman taimakonsa da samun nucuwa a duk lamarin da suka sa gaba da cewa : jagoranci da manufa ta marigayi Imam Khomeini ® shi ya taimakawa al'ummar Iran ga kuma riko da Addini da tafarkin manzon Allah (SWA) da limaman tsira (AS) kuma addinin musulunci shi ne addinin duniya da lahira.
361395