IQNA

Jam'iyar Labour ta kasar Norway ta bukaci da a gina wata cibiyar Horar dalimaman masallatai da masu wa'azi a cikin (jami'ar Auslo)

Kamfanin dillancin labaran Alkur'ani na kasar Iran Ikna ya nakalto daga jaridar Alwatan ta kasar Saudia cewa, 'yan jam'iyar Labour ta kasar Norway, sun bukaci kasashen musulmi da su hada gwiwa da gwamnatin kasar wajen gina wata cibiyar bayar da horo ga masu wa'azi na Musulunci da limaman masallatai.
Abdulmajid Jarrad daya ne daga cikin cikin 'ya'yan jami'iyar, kuma ya bayyana cewa mafi yawan masu wa'azi da limaman masallatai a kasar bas u da masaniya sosai kan al'adun mutanen kasar, wasunsu ma ba su ji yaren kasar yadda ya kamata.

Y ace samar da wta cibiya da za ta rika bayar da horo zai taimaka wajen samun masaniya kan al'adun kasar da kuma yadda musulmi za su gudanar da ayyukansu na addini ba tare da wata matsala ba, kuma hakan zai taimaka ma 'ya 'yan musulmi da aka Haifa a kasar, ta yadda za su iya koyon addini da yaren larabci a wannan cibiya.

363704