Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Yeman (sabanet) cewa, a cikin bayan bayan taro da aka karanta a karshen zaman, an jaddada wajabcin jingine tsattauran ra'ayi da wuce gonad a iri a cikin addini, domin ta hakan ne kawai za a iya fito da sahihiyar fuska ta addini Musulunci.
Ya zo a cikin bayanin bayan taron cewa, batun ijtihadi batu da ke bukatar fadada a kowane lokaci, kuma fadada shi ne fadada Musulunci ta dukkanin fuskoki, da hakan ya hada da banagaren fiqhu,Usul,ilimin zamantakewa, ilimin sanain halayyar dan adam da dai sauran mas'aloli na addini.
Sama dam asana 100 ne daga sassa daban-daban na kasashen musulmi suka halarci taron, ida suka hadu kan fadada bincike kan ilmomomin alkur'ani da littafai na ilimi da suka yi daidai da abin da zamani ke tafiya a kansa, tare da kiyaye mahangar addini a cikin kowane lamari.
Haka nan kuma dukkanin mahalartan sun sun hadu kan wajabcin karfafa yaren larabci a matsayinsa na yaren farko a addinin Musulunci, wanda kuma shi ne yaren alkur'ani da sunnar manzon Allah, kamar yadda mahalarta taron suka yi kira da a dauki matakai na hana yaduwar tunanin da ya yi karo da na addini a cikin al'ummar musulmi.
Taron ya tabo batun hare-haren ta'addancin da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan al'ummar Gaza, tare da yin kira ga kungiyoyin kare hakkin biladama na kasashen musulmi da na majalisar Dinkin Duniya, da su dauki matakai na shari'a kan shugabannin yahudawan sahyuniya, domin gurfanar da su a gaban kotun manyan laifuka ta duniya.
363857