Bangaren adabi: Wani malamin jami'a musulmi dan kasar Jamus, ya kwashe shekaru 40 yana kokarin sanar da kiristoci ma'anonin alkur'ani, ta yadda za su fahimci addinin musulunci da tsarkakan manufofinsa.
Cibiyar kula harkokin alkur'ani ta Iran Ikna, ta habarta cewa (Adel Ta'ur dour Khori) malamin jami'a dan kasar jamus, ya kwashe tsawon lokaci yana kokarin wayar da kan al'ummar kasar wajen bayyana musu fassarar alkur'ani, tare bayyana musu manufofin addinin musulunci sabanin yadda suka dauka, inda ya fassa alkur'ani mai tsarki a cikin yaren jamusanci, tare da yin Karin haske a kan ayoyi da dama da ke cikin alkur'ani da ke koyar da kyawawan dabi'u da kyautata mu'amala, da zamantakewar jama'a.
Wani masani bairaniye da ke zaune a kasar jamus (Ali Rahbar) ya bayyana cewa; Adel dan shekaru 79 ne da haihuwa, amma ya kwashe kimanin shekaro 60 yana hidima ga alkur'ani, tare da kokarin shiryar da mutane zuwa ga addini.
364409