IQNA

A Rasha An Kaddamar Da Baje Koli Kan Duniyar Musulunci Daga Cana Har Turai

Bangaren kasa da kasa: kasuwannin baje koli da sunan duniyar musulunci daga Cana har Turai a birin Kazan babban birnin jamhuriyar Tataristan mai cin gashin kansa a Rasha.
Bayan ta nakalto daga gidan talbijin na Rusiyal Yaum ,Cibiyar kula da harkokin Alkur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; a wannan kasuwar baje koli an kaddamar da abubuwa fahasa da kwarewa da hakan ke tabbatar da wayewar kasashen musulmi a tsawon tarihi musamman a lokacin da sauran kasashe hatta na turai ke cikin duhun jahilci da rashin wayewa. Kuma gidajen kollo da ajiyar kayan tarihi na Rasha da Faransa sun gamsu da amincewa da ci gaban da gidan ajiyar kayan tarihi na musulmi suka samu a tsawon tarihi.A wannan kasuwar baje koli an nuna yadda kasashen musulmi suka kasance cikin wayewa da ci gaba da yadda al'ummar musulmi suka kasance cikin ci gaba da wayewar a a fannoni daban-daban kamar kere-kere da gine-gine.

366717