Bangaren al'adu da fasaha: Hujjatul Islam da Musulmi Amiri wakilin jami'ar almustapha Al'alami (SWA) ya gana da tattaunawa da Cawiyat shugaban hadin guiwar kungiyoyin tattalin arzki da al'adu na Tailand.
Reshen cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikana a kudu maso gabacin Asiya ne ya watsa rahoton cewa: a wannan ganawa Cawiyat ya bayyana farin cikinsa a fili da cewa: hadin guiwar kungiyoyin tattalin arziki da al'adu na Tailan na farin ciki kuma a shirye suke su yi aiki kafada da kafada da jami'ar Almustapha (SWA) al'alami.Amiri wakilin jami'ar ta Almustapha (SWA) Al'alami shi ma ya nuna farin cikinsa da wannan ganawa tare da fatar ganin wannan hulda da dangantaka ta kut da kut da hadin guiwar kungiyoyin tattalin arziki da al'adu na kasar Tailand ya amfani duniyar musulmi.
368979