Bangaren likitanci: Musulunci ya bayyana wa musulmi halastaccen abinci da abin sha a cikin kur'ani, tare da bayyana musu wasu hanyoyi na tsara cin abincin, kamar yadda kuma ya bayyana musu wusu nau'oin abinci da aka haramta.
A wata zantawa da kamfanin dillancin labaran Ikna ya gudanar tare da bangaren kula da bincike kan ilmomin kur'ani, majiyar ta bayyana cewa kur'ani mai tsarki ya bayyana wasu abubuwa na ci wadanda suka halasta, tare da bayyana amfanin wasu daga cikinsu, kamar yadda kuma a wasu wuraren ya bayyana wasu nauo'in abinci wadanda haramun ne cinsu.
Majiyar ta ce; daga cikin abubuwan da aka halasta a cikin kur'ani kuwa hard a naman wasu dabbobi, kamar su shanu tumaki da awaki rakuma da dai sauransu, kamar yadda aka haramta cin naman wasu dabbobin, daga cikin kuwa hard a dabbobi masu dungu.
Jami'oin Iran na ayyukan likitanci suna gudanar da bincike kan wasu tsirrai da kur'ani ya mabata, inda tuni suka yi nisa wajen samar da magunguna ta hanyarsu.
370566