IQNA

Za A Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Kan Hadin Kan Musulmi Karo Na 22 A Tehran

Bangaren kasa da kasa: za a gudanar da taron kasa da kasa kan hadin kan musulmi a birnin Tehran kuma za a kwashe kwanaki uku.
Cibiyar kula da harkokin Alkur'ani a Iran Ikna ce ta nakalto daga bangaren hulda da jama'a na cibiyar kusancin mazhabobin musulunci ta bada labarin cewa: a wannan taro na kwanaki uku za a samu halartar wakilai daga kasashen Jamus,Britaniya,Indonoziya,Iraki,Labanon,Saudiya,Tailand, aljariya da wasu daga cikin masana da masu mukamin gwamnati da kula da bangaren ilimi da al'adu na kasashe 45 na duniya. A lokacin gudanar da wannan taro za a gabatar da makaloli da suka shafi yadda za a inganta hadin kan musulmi,da yadda ake haddasa rikici da ingiza rikici da rarrabuwa a tsakanin musulmi. Wasu kan jahici da ta'assubanci sunadadaga cikin makalolin da za a gabatar a gurin wannan taro na kwanaki uku.

37134