IQNA

An Girmama Wasu Shahidai Iraniyawa Uku A kasar Bosnia

Bangaren Fasaha: A wani taro da aka gudanar a kasar Bosnia kan shirye-shiryen fina-finai a kasar Bosnia, an girmama wasu shahidai Iraniwa su uku da suka yi shahada akasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a wani taro da aka gudanar a kasar Bosnia an girmama wasu shahidai Iraniya uku da suka yi shahada a kasar, wato (Mohammad Hossein Novab) da kuma (Behnam Niknam) da kuma (Rasul Haidari) wadanda sun yi shahada ne a lokacin da kasar ta fsukanci shishigi daga kasar Serbia, lamarin day a yi sanadiyar yin shahadar dubban mutane a kasar ta Bostania.
Wannan dai shi ne karo na uku da ake gudanar da irin wannan taro, wanda ke samun halartar masana daga kasar ta Bosnia na ciki da wajen kasar, inda ake girmama wadanda suka yi shahada ta hanyar nuna wasu fina-finai da aka shirya kan yakin da kuma irin ta'adin da sojojin Serbia suka yi wa al'ummar Bosnia.

373162