IQNA

Scottland Za Ta Dauki Bakuncin Taron Saka Hannayen Jari A Musulunce

Bangaren kasa da kasa: Scottland za ta daukin bakuncin taron manyan 'yan kasuwa musulmi da zai yi dubi kan batun saka hannayen jari a musulunce a cikin watan Afirilu mai kamawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-sharq Al-ausat) cewa; Scottland za ta daukin bakuncin taron manyan 'yan kasuwa musulmi da zai yi dubi kan batun saka hannayen jari a musulunce a cikin watan Afirilu mai kamawa, taron wanda na hadin gwiwa ne tsakanin babbar cibiyar harkokin kasuwanci da saka hannayen jari ta Scottland, da kuma kwamitin kula harkokin kasuwanci da saka hannayen jari na kasashen musulmi, za gudanar da shi a birnin Glasco fadar mulkin Scottland a farkon watan Afirilu mai kamawa.
Babbar manufar gudanar da taron dai ita ce gudanar da tattaunawa kan kayyaki da ake sana'antawa, da kuma matsayin addinin Musulunci a kansu, tare dad a duba yuwuwar yin aiki na hadin gwiwa wajen saka hannayen jari a abubuwan da dukkanin bangarorin suka amince da yin harka a kansu, musamman ma halastattun abubuwa a addinin Musulunci

379557